AMFANIN DABINO( DATE) A JIKIN DAN ADAM
FA'IDODIN DABINO A JIKIN DAN ADAM KU
DAURE KU KARANTA TABBAS ZAI AMFANEKU
•••••••••••••••••••••••••••••••••••
A yau ina so ne in kara wani bayanin kan
amfanin dabino a jikin dan adam, don wasu da
dama sun dauki dabino a
matsayin abin bude baki ne ga wanda ya kai
azumi ko kuma abin karin in’ima ga mata kawai.
.
To dabino ba nan kadai ya tsaya ba, ya ma fi
gaban hakan, don
kuwa yana abubuwan ban mamaki a
tatare da shi.
.
Bincike ya nuna dabino yana dauke da
sinadarin ‘bitamin B,’ wanda yake
taimakawa wajen baiwa cikin mutum
damar karbar abinci da zai biyo baya ba tare da
aikin ya samu matsala ba ko
rikicewa ba, shi ya sa ma Manzon Allah
(SAW) yake cewa, “Idan kun kai azumi,
to ku yi buda baki da dabino, amma idan
bai samu ba to ya yi amfani da ruwa,
domin ruwa na tsarkakewa.”
.
Haka kuma dabino yana dauke da sinadarin da
ke karawa jiki karfi da kwari, yana mayar da
sukari da ke cikin jinin mutum wanda yake
raguwa sakamakon rashin cin abinci ko abin sha,
dabino yana dauke da sinadarin ‘Iron,’ wanda
yake taimakawa wajen karin jini.
.
.
Sannan yana karfafa jini da hantar mutum.
.
Ga wasu daga cikin amfanin dabino ga dan
adam.
.
1. Yana samar da ruwan jiki
2. Yana taimakawa mata masu ciki
3. Yana karawa mai shayarwa ruwan nono
4. Yana gyara fatar jiki
5. Yana maganin ciwon kirji
6. Yana maganin ciwon suga
7. Yana maganin ciwon ido
8. Yana maganin ciwon hakori
9. Yana gyara mafitsara
10. Yana maganin basir
11. Yana kara lafiyar jarirai
12. Yana rage kiba, wadda ba ta lafiya
ba ce ma’ana kumburin jiki na ciwo
13. Yana maganin, majina
14. Yana sa kashin jiki ya yi karfi
15. Yana maganin gyambon ciki (Ulcer)
16. Yana kara karfi da nauyi
17. Yana maganin ciwo ko yanka
18. Yana karawa koda lafiya
19. Yana maganin tari
20. Yana maganin tsutsar ciki
21. Yana maganin kullewa ko cushewar
ciki
22. Yana rage kitse
23. Yana maganin cutar daji (Cancer)
24. Yana maganin cutar Asma (Asthma)
25. Yana kara karfin kwakwalwa
26. Yana maganin ciwon baya, ciwon
gabbai, ciwon sanyi wanda yake kama
gadon baya.
27. Yana kara sha’awa da kuzari
28. Yana magance cututtuka dake
damun kirji
29. Yana karya sihiri.
.
Bayan haka Al-Kur’ani mai girma ya yi
magana a kan dabino a wurare da dama
ga surorin da suke magana kan dabino,
ga surorin kamar haka.
.
1. Suratul Bakara, Aya ta 226
2. An’am, Aya ta 99 da 141
3. Suratul Ra’ad, Aya ta 4
4. Suratul Nahli, Aya ta 11 da 67
5. Suratul Isra’i, Aya ta 91
6. Suratul Kahfi, Aya ta 32
7. Suratul Maryam, Aya ta 23 da 25
8. Suratul Daha, Aya ta 71
9. Suratul muminin, Aya ta 19
10. Suratul Shu’ara, Aya ta 148
11. Suratul Yasin, Aya ta 34
12. Suratul Ka’af, Aya ta 10
13. Suratul Kamar, Aya ta 7
14. Suratul Rahman, Aya ta 11 da 68
15. Suratul Ha’akkah, Aya ta 7
16. Suratul Abasa, Aya ta 29
.
Wannan shi ya sa hatta a gidan fiyayen
halitta (SAW) ba abinci da ya fi dabino!
.
Domin cin dabinon Alkhairi Ne
.
••••••••••••••••••••••••••••••
.
Don't Forget Share
.
Godiya ga Allah da ya yi cuta ya yi mana
magani, kuma ya saukar mana abubuwa na yau
da kullum.
Allah ya kara mana lafiya. Wadanda ba su da ita
kuma Allah ya ba su,,,,,,,,
No comments