KWANKWASO YA FASA ZUWA KANO
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya fasa kai ziyarar da ya shirya kaiwa Kano gobe Talata.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda kauce wa rikicin siyasa da ka iya biyo bayan ziyarar tasa, kamar yadda Alhaji Rabi`u Sulaiman Bichi, mai magana da yawun bangaren kwankwasiyya .
Dan siyasar ya ce ya samu shawarwari daga bangarori da dama kan ya janye ziyarar.
A ranar Jumma'a ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta shawarci tsohon gwamnan da ya soke ziyarar da ya yi niyyar kaiwa jihar a ranar Talata 30 ga watan Janairu, saboda barazanar tashin hankalin da za a iya samu.
Akwai sabani mai tsanani tsakanin tsohon gwamnan da gwamna mai ci Abullahi Ganduje wadanda a da su kayi tafiya daya a siyasance.
No comments