Header Ads

Yan siyasan da ake sa ran za su tsaya takaran fidda gwani a jam'iyar PDP

Yan siyasan da ake sa ran za su tsaya takaran fidda gwani a jam'iyar PDP



- A cikin mutanen da ake sa ran za su tsaya takarar fid da gwani a jam'iyyar PDP akwai
 Atiku Abubakar
 da Sule Lamido
Ibrahim Shekarau


Hassan Dankwambo.
Ahmed Makarfi
 Yayin da zaben shugaban kasa Najeriya na shekara 2019 ya gabato, babban jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party PDP ta shiga cikin rudani akan wada za tsayar a matsayin dan takaranta. A shekarar da ta gabata ne jam’iyyar PDP ta ce, ta ba Arewacin kasa damar tsayar a dan takarar shugaban kasar Najeriya. A cikin mambobin jam’iyyar PDP da ake sa ran za su tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2019
Akwai tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, wazirin Adamawa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, Sanata Ahmed Makarfi tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsoho shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar PDP, tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da gwamnan jihar Gombe, brahim Hassan Dankwambo.


. Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar bai taba boye muradin sa na son yin shugabancin Najeriya ba, bayan haka ya sha tsayawa takara a Jam’iyyu dabam-dabam a kasar wanda ya hada. Wannan dalilin yasa ya kara canza sheka da jam’iyyar APC zuwa tsohuwar jam’iyyar PDP da ya ga alamar samun tikitin takara zai yi masa wuya a APC. Daga cikin masu yi.


2  Alhaji Sule Lamido 

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma tsohon ministan harkan kasar waje Sule Lamido, yana cikin manyan 'yan siyasan da suka kafa jam'iyyar PDP a Najeriya, kuma babu dan Arewan da ya fi shi dadewa a cikin jam’iyyar PDP. Lamido mutum ne da ya dauki shugabancin kasar nan da muhimmanci. Mutum ne da yake ganin zai iya gyara matsalolin da Najeriya ke fuskanta idan ya samu aka bashi damar yin shugabancin kasar. 


3. Ahmed Makarfi


Sanata Ahmed Makarfi ya taba gwaman jihar Kaduna na tsawon shekaru takawas kuma yayi sanata na shekaru takawas, bayan haka ya rike shugabanci kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar PDP na tsawon shekara daya. Ahmed Makarfi ya ganin manyan mukaman da ya rike kasar yasa ya cancanci yin shugaban cin kasar. A makon da ya gabata ne gungun matasan jam'iyyar PDP na jihar Kaduna suke roke shi ya fito takaran shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP za su mara mu shi baya.
4. Ibrahim Shekarau :


Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim shekarau ya kafa tarihi a siyasar jihar Kano inda ya zama gwamna na farko da aka zabe shi a karo na biyu a matsayin gwamna a jihar Kano. 

Shekarau yayi ministan a ilimi a lokacin shugabancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyar All Nigerian People's PartyANPP tare da Buhari, Jonthan da Ribadua zaben 2011 kafin ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP a shekara 2014. Ibrahim Shekarau yana daya daga cikin manyan ‘yan siyasan Arewa da ya nuna ra’yi tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
5. Ibrahim Hassan Dankwabo


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo yana cikin ‘yan siyasan Arewa da ake sa ran za su tsaya takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP. Dankwambo ya zama gwamnan jihar Gombe a shekara 2011, kuma ya kara tsaya takara karo na biyu a zaben 2015. Shi kadai ne gwamnan jam'iyyar PDP a yankin Arewa da ya kara dawowa kan kujerar sa bayan zaben 2015.


No comments

Powered by Blogger.